Tarzoma ta farke a karane bakhtari bayan jana'zar wani shahidi

17 Disamba 2014 - 12:37

Taskar labarai ta Abna ta lakanto cewa; bayan kare jana'zar wani saurayi da sojojin haramtaciyar kasar isra'il suka kashe mai suna mahmud Abdullah Adwan, matasan Falastinawa sun fada kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da kisan da sojojin sukayi ma matashin. Masu boren sun rika jifar sojojin haramtaciyar kasar da duwatsu wanda yasa sojojin maida martani da harba hayaki maisa hawaye da kuma harbi da harsashin roba.ABNA